Saturday, 24 January 2026

KALAMAN SOYAYYA

Kalaman Soyayya Masu Daɗi

Ya ke masoyiyata a gaskiya kina matukar burgeni da sani nishadi sosai a cikin raina. Ina matukar sonki.

Ya ke masoyiyar rayuwata, zuciyata bata taba cin karo da haddiyar tauraruwar da a kullum nake kwana da Son ta, sannan nake tashi da Begen ta ba sai ke kadai. Ina sonki.

Yake hadaddiyar masoyiyar rayuwata. Hakika bansan yadda zan miki bayanin irin So da Kaunar da zuciyata take miki ba. Abun da zan iya cewa kawai, gaskiya ina matukar Son ki.

My honey, idan kika dubi kanki a madubi, zaki ganki doguwa, kyakkyawa mai kyan siffar jiki, gaki kuma tauraruwar kyawawan matan duniya, a gaskiya kina matukar sanyaya min raina sosai kamar sanyin farin wata. I Love You

Samun ki a cikin rayuwata ya samar min da gagarumin canji da farin ciki, ta hanyar sauraren zazzakar muryarki da kuma kasance wata a tare da ke cikin rayuwarki mai tsari. Duk wani abun da zan furta a gare ki, bai wuce nace ina Son ki ba, Kuma soyayya ta agareki, soyayya ce ta gaskiya, ke ce tauraruwar da hasken ta yake haskaka birnin zuciyata, sannan kuma kina daya daga cikin mutanen da ba zan ta ba mantawa da su ba har abada a rayuwata.

Yake masoyiyata, yanayin kamun kanki yana matukar burgeni sosai. Ina matukar kaunarki a zuciyana. Sonki ya yabi jinin jiki na, ya lullube dukkan sassan zuciyata I Luv U

Duk da cewa kin sauya min fuska, amma ni, bazan taba sauya miki fuska ba, ballantana, har na faɗa miki abun da bai dace ba. Ina matuƙar sonki, masoyiyata

Sauran mutane suna bukatar numfashi domin suyi rayuwa, amma ni ke kadai kawai nake bukata don nayi rayuwa mai inganci. Ina matukar sonki, Masoyiyata

No comments:

Post a Comment